Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da buƙatar Nnamdi Kanu ta neman a kai shi asibiti, inda ta umarci ƙungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta kafa kwamitin likitoci tsakanin takwas zuwa goma domin tantance ainihin matsalar lafiyarsa.
Mai shari’a James Omotosho ne ya bayar da wannan umarni a yayin zaman kotu da aka yi ranar Juma’a, inda Kanu ya gabatar da buƙatar cewa ya kamata a mayar da shi ɗakin kulawa na musamman a asibitin ƙasa saboda yana fama da rashin lafiya mai tsanani.
Alƙalin ya bayyana cewa, kwamitin da NMA za ta kafa shi ne zai binciki lafiyar Kanu da kuma gano ko matsalolin lafiyar na iya hana shi ci gaba da fuskantar shari’a. Haka kuma, kwamitin zai tantance ingancin cibiyar kiwon lafiya ta Hukumar Tsaro ta DSS domin tabbatar da ko za su iya kula da shi yadda ya kamata.
Hukuncin ya kuma ƙunshi cewa kwamitin zai yanke shawara kan ko akwai buƙatar a kai Kanu babban asibiti kamar yadda ya nema, da kuma ko yanayin lafiyarsa zai iya zama cikas ga tsayuwarsa a gaban kotu.
Kotun ta kuma umurci babban daraktan asibitin ƙasa ko wakilinsa ya kasance cikin wannan kwamitin, tare da tabbatar da cewa shugaba da sakataren kwamitin sun saka hannu kan rahoton binciken da za a mika wa kotu cikin kwanaki takwas daga yau.