Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai mummunan hari a masallacin kauyen Yandoto, karamar hukumar Tsafe, a jihar Zamfara, da sanyin safiyar Juma’a.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kutsa cikin masallaci a lokacin da jama’a ke tsaka da sallar Asuba, inda suka bude wuta ba tare da jin tausayin masu ibada ba.
A cewar majiyoyi daga yankin, akalla mutane biyar sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata a harin. Wannan lamari ya girgiza al’ummar kauyen baki ɗaya, kasancewar ya faru ne a wurin ibada da ake ganin mafaka.
Shaidu sun bayyana cewa maharan ba su yi wata-wata ba, domin sun shiga cikin masallaci suka fara harbi kai tsaye, wanda ya jawo fargaba da rudani a tsakanin masu ibada.
Al’ummar yankin na ci gaba da nuna takaici da damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ta ƙaruwa a jihar Zamfara, lamarin da ke ƙara jefa jama’a cikin matsanancin tsoro da rashin tabbas.
Hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani ba kan wannan hari zuwa yanzu, sai dai rahotanni sun nuna ana sa ran daukar matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya a yankin.