Kwankwaso bai taba satar kudin Gwamnatiba – Buba Galadima

0
89

Wani jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Buba Galadima, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso, shi ne dan takarar shugaban kasa mafi farin jini kafin zaben 2023.

Galadima yace Kwankwaso yana da farin jinin lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Da yake magana a shirin safe na Arise News Galadima ya ce duk da cewa Kwankwaso ba shi da kudi domin bai taba satar kudin gwamnati ba, amma shi ne dan takarar da zai doke shi.

A cewar Galadima: “Dabararmu ita ce za mu nunawa ‘yan Najeriya cewa dan takara mafi farin jini idan zabe ya gudana shi ne Kwankwaso.

“Kwankwaso ba shi da kudin da zai yi yakin neman zaben shugaban kasa saboda bai saci dukiyar jama’a ba.

“Kowa a fadin duniya ya san cewa Kwankwaso ne dan takarar da ya fi farin jini a doke shi, Kwankwaso yana da sihirin da zai magance matsalolin ‘yan Najeriya.”

Ya kuma caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan karramawar da aka yi wa ‘yan Najeriya.

Galadima ya ce ya kamata a ce yawancin wadanda aka karrama sun kasance a gidan yari.

Ya kara da cewa “Mutane 440 da Buhari ya ba lambar yabo ta kasa su kasance a gidan yari, a bayar da wadannan kyaututtukan ga mutanen da suka yi ritaya ba tare da wata aibu ba.”