Majalisar Shura ta jihar Kano zata yi nazari akan kalaman Malam Lawan Triumph

0
28

Majalisar Shura ta jihar Kano zata yi nazari akan kalaman Malam Lawan Triumph 

Gwamnatin jihar Kano ta mika takardun ƙorafi da kuma martani daga ƙungiyoyin addini kan kalaman malamin addini, Sheikh Lawan Triumph, zuwa ga Majalisar Shura domin duba su.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sakataren gwamnatin jihar, Musa Tanko, ya fitar, an bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince a mika batun domin a yi nazari da shawara kan lamarin.

Ƙungiyoyin da suka mika ƙorafi sun haɗa da:

Safiyatul Islam of Nigeria

Tijjaniya Youth Enlightenment Forum

Interfaith Parties for Peace and Development

Sairul Qalbi Foundation

Habbullah Mateen Foundation

Imaman Masallatan Juma’a na Qadiriyya Movement

Kwamitin Malaman Sunnah a Kano

Multaqa Ahbab Alsufiyya

Sakataren gwamnatin jihar, Umar Farouk Ibrahim, ya bayyana cewa an umarci majalisar ta Shura da ta yi nazari mai zurfi sannan ta ba da shawara a kan wannan cece-kuce.

Ya kuma ƙara da cewa:

> “Gwamnatin jihar Kano na nan daram kan manufarta ta tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da girmama juna tsakanin dukkan ƙungiyoyin addini.”

Daga ƙarshe, gwamnatin ta roƙi jama’ar jihar da su kwantar da hankali tare da bin doka da oda yayin da ake nazari a kan wannan batu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here