Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta bayar da umarni ga dukkan mambobinta da su dakatar da aiki daga yau, lamarin da zai iya jefa kasar nan cikin matsalar samar da wutar lantarki.
A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta bayyana cewa dalilan wannan yajin aiki sun haɗa da:
Rashin biyan albashin ma’aikata tun daga watan Afrilu 2025.
Gazawar gwamnati wajen aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi.
Rashin samar da kayan aiki da na kariya.
Kin biyan hakkokin fansho.
Da kuma cigaba da riƙe ma’aikata a matsayin na ɗan lokaci ba tare da daidaita matsayinsu ba.
Hakan na iya janyo katsewar wuta a sassa daban-daban na ƙasar nan musamman a wuraren da aka samu ɗan ci gaba wajen samun wutar tun bayan ƙarin kuɗin lantarki a bara.
Jama’a dai na fargabar cewa matsalar zata tsananta idan gwamnati da kungiyar ba su cimma matsaya cikin gaggawa ba.


