Saudiyya ta gindaya sharuɗa masu tsauri ga maniyyatan hajjin shekarar 2026

0
69

Mahukuntan kasar Saudiyya sun gabatar da sabbin tsauraran ka’idoji ga alhazai na Hajji shekarar 2026, abin da ya sa hukumar kula da harkokin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta yi gargaɗi saboda yiwuwar rashin damar zuwa aikin hajji ga wasu daga cikin maniyyatan Najeriya.

Fatima Sanda Usara, mai rikon mukamin Daraktar Yada Labarai ta NAHCON, ta shaida wa BBC cewa babbar manufar Saudiyya ita ce: duk wanda bai kammala biyan kuɗin Hajji ba kafin wa’adin da aka ƙayyade ba za a karɓi biyan kuɗin sa daga baya ba. An bayyana cewa dole ne a kammala dukkan shirye-shirye, musamman waɗanda suka shafi harkokin sufuri da kwangiloli a Saudiyya, kafin 12 ga watan Oktoban 2025.

Usara ta ƙara da cewa daga bangaren kiwon lafiya, an ƙayyade cewa duk mai niyyar zuwa Hajji zai gabatar da tabbacin cewa yana cikin koshin lafiya. Wadanda ke da cututtuka masu tsanani kamar ciwon koda, ciwon hanta, cututtukan da za a iya yadawa (misali tarin fuka, Ebola, zazzabin Lassa) da masu tabin hankali ko masu juna biyu za su iya rasa damar zuwa idan an tabbatar da alamun cutar. Duk da haka, an ambaci cewa cututtuka kamar hawan jini da ciwon siga ba su cikin jerin hana tafiya idan mutum na tafiya da maganinsa da shaidar ciwon.

Mahukuntan Saudiyya sun bayyana waɗannan matakan ne don su san ainihin adadin alhazai daga kowacce ƙasa domin a yi tanadi na kulawa da sufuri a lokacin gudanar da aikin Hajji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here