PDP ba za ta iya cin zabe ba idan na fice – Wike

0
89

Yayin da rikicin jam’iyyar PDP ke ci gaba da kara kamari, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce jam’iyyar ba za ta iya lashe zaben shugaban kasa a 2023 ba.

Wike ya ce shi da wasu gwamnoni hudu suna taka muhimmiyar rawa a PDP; don haka jam’iyyar ba za ta iya cin zabe ba tare da su ba.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Fatakwal, babban birnin jihar a ranar Juma’a.

Wike, Samuel Ortom na jihar Benue, Seyi Makinde na jihar Oyo, Okezie Ikpeazu na jihar Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, sun yi ta kiraye-kirayen a tsige Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Gwamnonin sun dage cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da shugaban kasa, Ayu ba za su iya fitowa daga yanki daya ba.

Sai dai Wike ya ce shi da tawagarsa sun himmatu wajen yin tasiri a jam’iyyar.

A cewar gwamnan PDP ta lashe wasu jihohin ne saboda tallafin da ya ke bayarwa.

“Idan na bar jam’iyyar a yau, PDP ba za ta iya cin zabe ba. Idan gwamnonin PDP biyar suka ce yau za su tafi, mu ba gwamnonin talakawa ba ne, muna da jajircewa da karfi.