Zamu ɗauki mataki akan Malam Lawan Triumph bayan karɓar ƙorafi akan sa–Gwamnan Kano

0
118

A Kano, wasu daga cikin al’umma sun fito zanga-zangar lumana kan zargin kalaman da malamin addini, Sheikh Lawan Abubakar Triumph, ya yi kan Annabi Muhammadu (SAW).

Masu zanga-zangar sun isa gidan gwamnatin Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarɓe su tare da yi musu jawabi.

Lamarin ya samo asali ne daga wani bidiyo da ya yadu a baya-bayan nan, inda aka ji malamin yana musanta cewa haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) da kaciya wani al’ajabi ne, yana mai cewa ruwayoyin da suka kawo haka ba su da inganci.

Da yake magana da masu zanga-zangar, Gwamna Abba ya roƙe su da su kwantar da hankali, tare da basu tabbacin cewa gwamnati za ta ɗauki matakin da bai saɓa wa Shari’a ba. Ya kuma bukace su su gabatar da takardar koke a hukumance ta hannun ofishin sakataren gwamnati.

Masu zanga-zangar sun amince da wannan umarni, inda suka tsara kai takardar da gwamnan ya nema da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar Alhamis.

Abba, yace gwamnati zata yi duba akan bukatar masu zanga-zangar da kuma ɗaukar matakin da ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here