Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS), Zacch Adedeji, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ciyo bashi duk da samun ƙarin kuɗaɗen shiga a watannin baya-bayan nan.
Adedeji ya ce ɗaukar bashi ba alamar rauni ba ne, illa kawai wani ɓangare na dabarun tattalin arzikin ƙasa. Ya bayyana cewa a watan Satumba 2025, FIRS ta tara harajin da ya kai Naira tiriliyan 3.64, wanda ya ninka da kashi 411 cikin ɗari daga Naira biliyan 711 da aka tara a Mayu 2023.
Sai dai wannan na zuwa ne bayan kusan wata biyu da Shugaba Bola Tinubu ya nemi aron $21.5bn daga kasashen waje, ciki har da bashi na $2bn da kuma N757.98bn don biyan bashin fansho.
A baya-bayan nan, gwamnatin Tinubu ta sha suka daga masana da ‘yan ƙasa kan yadda take ta dogaro da bashi duk da samun karuwar kudaden shiga.