Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da wani shiri na tsawaita mulkinsa bayan wa’adinsa na doka, idan ya sake lashe zaɓen 2027.
Wannan na zuwa ne bayan tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya kwatanta gwamnatin Tinubu da ta Paul Biya na Kamaru, wanda ya daɗe kan mulki tun daga 1982.
A wata sanarwa da mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan dabarun yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce maganganun El-Rufai “ba su da tushe kuma ba su da ma’ana.” Ya ƙara da cewa Tinubu mai goyon bayan dimokuraɗiyya ne kuma zai kammala mulkinsa a ranar 28 ga Mayu, 2031, idan ya sake cin zaɓen 2027.
El-Rufai dai ya yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu na mayar da ikon ƙasa hannun gwamnati ɗaya, wanda a cewarsa, barazana ce ga tsarin dimokuraɗiyya. Haka kuma ya yi gargadin cewa idan ba a dakatar da wannan salon mulki ba, Tinubu zai iya zama “Paul Biya” na Najeriya.
Sai dai Onanuga ya nuna cewa El-Rufai ya faɗi hakan ne saboda rashin nasarar shirin jam’iyyarsa (ADC) na ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027, inda ya ce goyon bayan da Shugaban Ƙasa ke samu musamman a Arewacin Najeriya ya karya hujjojin El-Rufai.