Kashim Shettima zai wakilci Tinubu a taron majalisar ɗinkin duniya

0
105

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja a ranar Lahadi zuwa birnin New York, Amurka, domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaman taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80.

A wata sanarwa da ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya fitar ta hannun mai taimaka masa a harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, an bayyana cewa Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a babban taron.

Taron zai gudana daga Litinin, 22 ga Satumba, zuwa Lahadi, 28 ga Satumba, 2025. Shettima zai kuma halarci tattaunawar manyan shugabanni da sauran muhimman taruka a gefen babban zaman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here