Shugabannin ƴan bindiga sun yi alkawarin zaman lafiya a Katsina

0
99

A ranar Asabar data gabata ne shugabannin ƴan bindiga a wasu yankuna na Jihar Katsina suka halarci taron zaman lafiya da aka shirya a ƙananan hukumomin Sabuwa da Matazu, ƙarƙashin shirin gwamnatin tarayya na Operation Safe Corridor.

Rahoton masanin harkokin tsaro Zagazola Makama ya bayyana cewa tarurrukan sun haɗa shugabannin al’umma, jami’an gwamnati da kuma shugabannin ƴan bindiga.

A Sabuwa, taron ya gudana a ƙauyen Dugun Muazu, inda shugaban ƙaramar hukumar Sagir Tanimu, ɗan majalisar jiha Ibrahim Danjuma da wasu dattawan al’umma suka halarta. A ɓangaren ƴan bindiga kuma, sun haɗa da Kabiru, Maisaje, Kachalla Adamu Risku da wasu da dama.

Haka nan a Matazu, taron ya gudana a makarantar firamare ta Yargeza, karkashin jagorancin shugaban ƙaramar hukumar Shamsuddeen Sayaya da hakimin yankin. Shugabannin ƴan bindiga da suka halarta sun haɗa da Muhammadu, Sani Yellow da Ummaru Manore ta hannun wani mai shiga tsakani.

Dukkan ɓangarorin biyu sun jaddada aniyar su na daina fada da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Jami’ai sun ce za a ci gaba da tattaunawa da shugabannin al’umma domin ƙarfafa wannan sabon shirin zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here