Jami’ar European-American ta ce digirin girmamawar Rarara na bogi ne

0
74

Jami’ar European-American ta karyata labarin cewa ta karrama fitaccen mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara, da digirin girmamawa, tana mai bayyana wannan batu a matsayin damfara.

Wannan karin haske ya biyo bayan rahotanni da suka bayyana cewa an yi bikin bayar da digiri a babban dakin taro na Nicon Luxury Hotel Abuja, inda aka ce Rarara tare da wasu mutane sun samu lambar girmamawa a gaban manyan baki ciki har da gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda.

A wata sanarwa da jami’ar ta wallafa a shafinta, ta ce ba ta da hannu ko izini a wannan biki, kuma wadanda suka gabatar da kansu a matsayin wakilan jami’ar sun aikata hakan ne ba tare da yardar ta ba.

> “Jami’ar ba ta amince a gudanar da wani bikin karramawa a wannan lokaci da wurin da aka ce an yi shi ba. An shirya wannan taro cikin yaudara, ba tare da sani ko izinin jami’ar ba,” in ji sanarwar.

Haka kuma, jami’ar ta nesanta kanta da wasu mutane da suka yi ikirarin cewa su mambobin majalisar gudanarwarta ne a Najeriya, ciki har da Idris Aliyu da Musari Audu Isyaku, tana mai cewa duk wata alaka da su an soke ta.

Sanarwar ta kara da cewa shugaban jami’ar a yanzu shi ne Farfesa Luca Scotto di Tella de’ Douglas di Castel di Ripa, ba Dr. Josephine Egbuta ba wadda aka riga aka tsige saboda laifin rashin da’a ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here