Mummunar fashewa ta afku a wajen ƙera makaman sojoji dake Kaduna

0
85

Mummunar fashewa ta afku a wajen ƙera makaman sojoji dake Kaduna

Wata babbar fashewa ta auku a Kamfanin Kera Kayan Yaƙin Soja na Najeriya da ke Kakuri a birnin Kaduna a ranar Asabar. Lamarin ya jawo mutuwar mutum ɗaya tare da raunata mutane da dama.

Shaidu sun bayyana cewa ƙarar fashewar ta girgiza sassan birnin, musamman a Chikun da kuma Kudancin Kaduna, inda jama’a da dama suka firgita.

Mutanen da suka jikkata an garzaya da su zuwa asibitocin gwamnati, ciki har da babban asibitin sojoji da ke Kaduna domin samun kulawa.

Har yanzu hukumomi ba su bayyana musabbabin wannan fashewar ba, sai dai sun tabbatar da cewa an fara gudanar da bincike domin gano dalili da kuma adadin barna da ta jawo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here