Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya isa Kaduna a yau Juma’a domin halartar ɗaurin auren Nasirudeen Yari, ɗan tsohon gwamnan Zamfara kuma Sanata Abdulaziz Yari.
Bayan haka, fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban zai yi amfani da wannan ziyarar wajen kai gaisuwa ga iyalan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da ke Kaduna.
Tinubu ya kuma gudanar da sallar Juma’a tare da jama’a a masallacin Sultan Bello da ke cikin birnin Kaduna kafin daurin auren.