Hukumomin jihar Bauchi sun tabbatar da mutuwar akalla mutum 58 sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a ƙananan hukumomi 14 daga cikin 20 na jihar.
Rahotanni sun nuna cewa sama da mutum 258 aka tabbatar sun kamu da cutar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito daga bakin Mataimakin Gwamnan jihar, Auwal Mohammed Jatau, yayin wani taron da aka gudanar a ranar Alhamis.
Mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake kaddamar da kwamitoci biyu da za su jagoranci yaƙi da annobar a jihar.
A cewarsa, “Kwalara cuta ce da za a iya kaucewa idan aka tabbatar da tsaftar ruwan sha da tsaftar muhalli da jiki.”