Tinubu zai ziyarci iyalan marigayi Buhari a Kaduna

0
25

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar yini ɗaya a Kaduna ranar Juma’a, 19 ga Satumba, 2025. A cewar mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, shugaba Tinubu zai halarci bikin ɗaurin auren Nasirudeen Yari, ɗan Sanata Abdul’aziz Yari, da Safiyya Shehu Idris.

Bayan haka, shugaban zai kai gaisuwar ban girma ga Aisha Buhari, matar marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a gidan marigayin da ke Kaduna.

Tinubu zai koma Abuja a wannan rana bayan kammala ziyarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here