Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta raba Naira biliyan 330 ga marasa karfi a fadin kasar nan.
Ministan Kudi Wale Edun, ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya ce sama da gidaje miliyan 19.7 da mutane kusan miliyan 70 ne ke cikin rijistar talakawa ta kasa.
Ya ce an fara biyan gidaje miliyan 8.5 daga cikin wadanda suka cancanta, inda kowane gida ke karbar Naira 25,000 cikin matakai daban-daban, kuma sauran za su samu nasu kason kafin karshen shekara.
Edun ya kara da cewa tsarin yana amfani da NIN da kuma asusun banki domin tabbatar da gaskiya da tsaro wajen rabon kudin.
Ya ce shirin yana daga cikin dabarun shugaban kasa Bola Tinubu na rage radadin cire tallafin mai da kuma tsadar rayuwa, kuma daga yanzu za a rika ware masa kudi a cikin kasafin kudin kowace shekara.