Yan Sandan Lagos sun fara binciken bidiyon ɗaliban makaranta suna shan taba da giya

0
19

Yan Sanda sun Lagos ta fara binciken bidiyon ɗaliban makaranta suna shan taba da giya

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Lagos ta fara cikakken bincike kan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta inda aka ga wasu ɗaliban Excel College, Ejigbo, suna shan taba, giya da kuma rawa a cikin ɗakin kwanan makaranta.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru tun a watan Afrilu 2025 a ɗakin kwanan samari na makarantar, amma sai dai ya sake bayyana a yanar gizo a wannan makon, lamarin da ya jawo fushin iyaye da al’umma da dama, tare da suka kan yadda ake sakaci wajen kula da ɗalibai a makarantu.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Olohundare Jimoh, ya umurci Sashen Binciken Manyan Laifuka na Panti da su karɓi alhakin binciken daga ofishin ‘yan sanda na Ejigbo, wanda tun farko ya gayyaci shugaban makarantar don amsa tambayoyi.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abimbola Adebisi, ta bayyana a cikin wata sanarwa ranar Alhamis cewa shugaban makarantar, ya tabbatar cewa ɗaliban da suka fito a cikin bidiyon sun riga sun kammala karatunsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here