Tinubu ya dakatar da dokar ta-baci a Rivers

0
22

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da dokar ta-baci da aka kafa a Jihar Rivers.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, shugaban ya umarci gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, wanda aka dakatar, da ya koma bakin aiki daga gobe Alhamis, 18 ga Satumba.

Tinubu ya kuma ba da umarni ga mataimakiyar gwamna, Ngozi Nma Odu, tare da ‘yan majalisar dokokin jihar, da su koma bakin aikinsu nan take.

An bayyana dokar ta-bacin a jihar kimanin watanni shida da suka gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here