Libya ta kama yan Najeriya mazauna ƙasar ba bisa ka’ida ba

0
174

Hukumomin ƙasar Libiya sun fara mayar da ‘yan Najeriya 18 da aka kama ba tare da takardun zama ba daga cibiyar tsare baki ta Sirte zuwa garin Sabha da ke kudancin ƙasar, inda ake sa ran za a turo su Najeriya a cikin kwanaki masu zuwa.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ƙungiyar Migrant Rescue Watch ta fitar a ranar Litinin, inda ta ce jigilar ta gudana ƙarƙashin kulawar hukumar yaƙi da baƙin haure ta Libiya (DCIM), tare da rakiyar jami’an tsaro.

Rahoton ya nuna cewa an cafke mutanen ne a yayin da suke ƙoƙarin tsallaka Tekun Bahar Rum zuwa Turai ta hanyar da ba ta dace ba.

A cewar majiyoyi, za su ci gaba da kasancewa a cibiyar tsare baki ta Sabha har sai an kammala shirye-shiryen tura su Najeriya.

Kasashen duniya da dama da kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun sha bayyana damuwa kan cunkoson jama’a, rashin ingantattun yanayi da kuma cin zarafin da ake fuskanta a irin waɗannan cibiyoyin tsare baki a Libiya.

Duk da dogon lokaci na rikice-rikicen siyasa da yaƙe-yaƙe da suka addabi Libiya, ƙasar ta ci gaba da zama babbar hanya ga ‘yan gudun hijira da ke ƙoƙarin ketarawa zuwa Turai ta Bahar Rum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here