Ƙungiyoyin ma’aikatan jami’o’i a Najeriya, SSANU da NASU, sun baiwa gwamnatin tarayya wa’adin mako guda domin ta biya bukatun su ko kuma su tsunduma yajin aiki.
A wata wasiƙa da suka aika wa Ministan Ƙwadago, Muhammad Dingyaɗi, ƙungiyoyin sun ce idan gwamnati ta gaza warware matsalolin da suke ciki, za su fara yajin aiki bayan karewar wa’adin.
Bukatun su sun haɗa da biyan alawus da ya kai Naira biliyan 50, albashin da aka riƙe musu, da kuma cikon ƙarin albashin kashi 25/35. Haka kuma sun zargi gwamnati da kin cika yarjejeniyar da aka cimma tun 2009.
Wa’adin ya fara aiki daga Litinin, 15 ga Satumba, 2025, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.