Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa da ke ƙarƙashin Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a ranar Litinin.
Wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da ƙungiyar ta fitar a yau Litinin, wacce shugaban ta, Dr. George Ebong, tare da sakataren sa, Dr. Agbor Affiong, suka sanya wa hannu.
Ƙungiyar ta ce ta dauki wannan mataki ne bayan kammala yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai da ta fara a makon da ya gabata, sakamakon gaza cimma matsaya da hukumomin Abuja, duk da tattaunawar da aka gudanar mai tsaho.