Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Dr. Faruk Umar Faruk, ya bayyana inda yake so a binne shi idan ya rasu.
Sarkin ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake tare da tsohon Gwamnan Jigawa, Dr. Sule Lamido, tsohon hafsan tsaro Janar Aliyu Gusau (rtd), da fitaccen ɗan kasuwa Alhaji Dahiru Barau Mangal, Ajiyan Katsina, da wasu manyan baki.
A yayin ziyarar, Sarkin ya jagorance su zuwa kaburburan tsoffin sarakunan Fulani da suka mulki Daura, ciki har da na Marigayi Sarki Muhammad Bashar, Sarki Abdurrahman da Sarki Mallam Musa. A nan ne ya kuma nuna wajen da ya ke so a binne shi idan Allah Ya yi masa rasuwa.
An kuma gudanar da addu’o’i na musamman domin neman rahama da gafara ga waɗanda suka rigaya mu gidan gaskiya tare da fatan Allah Ya kyautata makomar dukkan musulmi.