Gaskiya Ko Jita-jita? Rahoton Cewa Wike Ya Kamu Da Ciwon Zuciya
Wasu kalamai sun yadu a shafukan sada zumunta, inda aka ruwaito cewa Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, na fama da ciwon zuciya mai tsanani a Birtaniya.
Rahoton da aka danganta da Sahara Reporters ya ce wasu majiyoyi sun tabbatar musu cewa Wike na karɓar kulawar likitoci a can bayan gano yana fama da cutar. Sai dai, babu wata kafa mai inganci da ta tabbatar da wannan ikirari.
Dalilin jita-jitar
An lura cewa tun daga 3 ga Satumba, lokacin da Wike ya halarci bikin kaddamar da aikin gyaran titin Karu Interchange a Abuja, bai sake bayyana a bainar jama’a ba.
Tun daga lokacin, wasu daga cikin manyan jami’ansa suka rika wakiltarsa a taruka da dama:
4 ga Satumba: Chidi Amadi, shugaban ma’aikata, ya wakilce shi wajen rabon taki a FCT.
11 ga Satumba: Ƙaramar ministar Abuja Mariya Mahmud Bunkure, ta wakilce shi a taron shekara na likitocin yara a Abuja.
Wannan rashin bayyana a fili ya ƙara haifar da jita-jitar cewa ministan yana jinya a ƙasashen waje.
Shiru daga bangaren Wike
Mai magana da yawun sa, Lere Olayinka, wanda ya saba gaggauta karyata labaran da ba daidai ba, bai ce uffan ba kan wannan batu.
Yanzu dai al’umma na jiran bayani kai tsaye daga bangaren Wike ko ofishinsa domin tabbatar da gaskiyar wannan rahoto da ke cigaba da yawo a shafukan sada zumunta.
Idan za’a iya tunawa ko a watannin baya an riÆ™a yaÉ—a jita-jitar rashin lafiyar Wike, sai dai daga baya an samu tabbacin cewa wannan labari ba gaskiya bane.