Duk da ƙoƙarin gwamnati da tura jami’an tsaro da dama, jihar Sokoto na ci gaba da fuskantar matsanancin hare-haren ’yan bindiga da suka addabi mutane a kananan hukumomi 10, inda suka bar gidaje ƙurmus, jama’a cikin makoki da dubban ’yan gudun hijira.
A Sabon Birni, mahaifar mataimakin gwamnan jihar Idris Mohammad Gobir, ’yan bindiga na kai farmaki da dare, suna ƙona gidaje, sace mutane da kwasar dukiya. Haka ma a Isa LGA, inda garuruwa kamar Bafarawa da Kamarawa suka zama tamkar karkashin ikon ’yan ta’adda, suna kai hari a rana tsaka tare da kafa shingen hanya don yin garkuwa da matafiya.
A wasu yankuna kamar Goronyo, Wurno, Rabah, Tureta da Dange/Shuni, maharan na amfani da dabarun yaki na ƙwanton bauna, suna lalata shaguna da kwasar abinci. A Illela, Tangaza, Gudu da Binji kuwa, hare-haren sukan faru da tsakar dare, inda suke kashe jama’a cikin gidajensu tare da ƙona kauyuka baki ɗaya.
Matsalar ta janyo mummunan rikicin jinƙai, inda dubban mutane suka rasa muhallansu, gonaki suka lalace, makarantun yara kuma suka tsaya cik.
Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Col. Ahmed Abdul Usman (rtd), ya bayyana cewa matsalar babba ce, ba wai ’yan bindiga kawai ba ne, illa masu ba su bayanai da ke cikin al’umma.
Gwamna Ahmed Aliyu ya gargadi cewa duk wanda aka kama yana taimaka wa ’yan bindiga ko kuma ya nemi fansar masu ba da bayanai, za a hukunta shi ba tare da sassauci ba.
Domin ƙara ƙarfin jami’an tsaro, gwamnatin jihar ta raba sabbin motocin Hilux 14 da babura 100, tare da tallafa musu da mai da kuɗin alawus. An kuma kafa rundunar masu tsaron gari don haɗa kai da jami’an tsaro.
Sai dai duk da waɗannan matakai, al’ummar karkara a Sokoto na ci gaba da rayuwa cikin fargaba.