Sojoji sun ce sun kashe ɗan ta’adda Babangida Kachalla

0
22
Sojoji
Sojoji

Sojojin Rundunar 12 Brigade ta Najeriya tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro a ƙarƙashin Operation ACCORD III sun samu nasarar kashe wani shahararren shugaban ’yan ta’adda, Babangida Kachalla, a dajin Ofere da ke jihar Kogi.

Mai magana da yawun rundunar, Lt. Hassan Abdullahi, ya bayyana cewa, a ranar 11 ga Satumba 2025, bayan samun sahihin bayani kan motsin ’yan ta’adda a yankin Ofere da Ayetoro Gbede, sojoji suka yi shirin kama masu laifin.

Duk da cewa ba su samu damar kai farmaki ba a farkon yunƙurin, yayin dawowa sansani sai ’yan ta’addan suka yi musu kwanton bauna. A fafatawar da ta biyo baya, sojoji sun yi nasarar fatattakar su tare da kashe ɗaya daga cikin su.

A yayin bincike a wurin, sojojin sun gano:

Harsasai,

wayoyi 31,

na’urar duba hawan jini,

kwayoyin Tramadol,

kayan tsafi,

da kuɗi Naira 16,000.

Rahotannin bayan bincike sun tabbatar da cewa Babangida Kachalla, wanda shi ne na biyu ga jagoran wata kungiyar ’yan ta’adda mai suna Kachala Shuaibu, ya jikkata sosai a harin kuma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here