An samu sabon salon rikicin da ke tsakanin Kamfanin Mai na Dangote da Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Najeriya (NUPENG), inda kamfanin Dangote ya kalubalanci kungiyar da ta bayyana wadanda suka batar da dala biliyan 18 da aka ware domin gyaran Matatun man gwamnati da suka gaza dawowa aiki.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, Dangote ya tambayi dalilin da yasa masana’antun man gwamnati a Fatakwal, Warri da Kaduna suka ci gaba da zama babu aiki, duk da kudi masu yawa da ake cewa an kashe wajen gyara su tsawon shekaru.
Alhaji Aliko Dangote ya ce tun daga shekarar 2007, an kashe makudan kudade kan gyaran masana’antun, amma har yanzu ba su dawo aiki ba. Dangote ya kuma tunatar da cewa a lokacin da aka yi yunƙurin sayar da masana’antun Fatakwal da Kaduna ga wani kamfani da ya haɗa da kamfanin sa, NUPENG ce ta yi ƙarfi wajen hana hakan, ta kuma bukaci a soke sayarwar.
Dangote ya ce:
“Lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su fara tambayar me ya faru da wadannan kudade da kuma dalilin da yasa masana’antun gwamnati suka gaza aiki duk da batar da irin wannan arziki.”
A gefe guda, kamfanin ya mayar da martani kan zargin da NUPENG ke yi na cewa yana neman mamaye harkar rarraba man fetur a kasar. Dangote ya ce matatar sa na aiki ne a tsarin kasuwar da aka sake bude ta (deregulated market), karkashin kulawar Hukumar Tsare-tsaren Harkokin Man Fetur ta Kasa (NMDPRA).
A ranar Juma’a, Ma’aikatar Kwadago ta kira wani taro domin sasanta sabuwar matsalar tsakanin bangarorin biyu, inda aka gudanar da zaman a ofishin Hukumar Tsaro ta (DSS) a Abuja.