Likitoci sun shiga yajin aiki a faɗin Najeriya

0
19

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta ƙasa (NARD) ta fara yajin aiki na gargadi na tsawon kwana biyar daga yau Juma’a, 12 ga Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan ƙarewar wa’adin da suka bawa gwamnatin tarayya kan batutuwan da suka shafi bashin albashi, kuɗaɗen alawus da kuma batun jin daɗin ma’aikata.

A wata sanarwa da sakataren kungiyar, Dr. Oluwasola Odunbaku, ya fitar, ya tabbatar da cewa dukkan cibiyoyi an umarce su da su ja hankalin mambobinsu kan fara yajin aikin da karfe 8:00 na safiyar yau.

Daga cikin korafe-korafen da suka gabatar akwai:

Rashin biyan kuɗaɗen horon likitocin na shekarar 2025.

Bashin watanni biyar na sabon tsarin albashi.

Rashin biyan kuɗin alawus na musamman.

Kungiyar ta ce matakin ya biyo bayan taron gaggawa da aka yi na tsawon sa’o’i shida, bayan gwamnatin ta gaza cika alkawuran da aka daɗe ana jira duk da tsawaita wa’adin sau biyu wanda ya ƙare a ranar 10 ga Satumba.

NARD ta bayyana cewa sun shiga yajin aiki ne saboda ƙin kulawar gwamnati ga batutuwan da suka shafi jin daɗin likitoci, lamarin da zai iya haifar da matsala ga harkar kiwon lafiya a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here