Mun tattauna da Goodluck akan matsalolin da Najeriya ke ciki–Peter Obi

0
18

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya gana da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, a Abuja ranar Alhamis.

 Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa Jonathan na iya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Sai dai, a wani saƙo da Obi ya wallafa a shafinsa na X bayan taron, ya bayyana tattaunawar a matsayin ta “sirri”, inda ya ce: “Na yi ganawa da yayana, dattijo kuma shugaba, kan halin da ƙasar mu ke ciki.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here