Kano: Gwamnati ta nemi majalisa ta haramta duk wani abu da ya shafi auren jinsi

0
4

Gwamnatin Kano ta nemi majalisar dokokin jihar ta yi dokar da za ta haramta dukkan wani abu da ya shafi auren jinsi da dangoginsa a fadin jihar.

Matakin ya biyo bayan zaman majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a ranar Laraba, inda aka amince da mika bukatar ga majalisar dokoki domin aiwatar da ita.

Kwamishinan Kasa da Safiyo na Kano, Abduljabbar Mohammed Umar, shi ne ya rattaba hannu kan kudurin kafin a mikawa majalisar dokoki, inda ya ce gwamnati na son ganin an samu doka ta musamman da za ta dakile duk wata alaka ko aiki da ya shafi lamarin auren jinsi.

Kano na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke amfani da tsarin shari’ar Musulunci, wanda a karkashin ta aka haramta auren jinsi tare da tanadar hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama da laifin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here