Gwamnatin Jihar Kano ta amince da sauya matsugunin kasuwar ‘Yan Lemo daga Na’ibawa zuwa kasuwar Dangwauro, domin kara inganta tsaro da walwalar al’umma.
Kwamishinan Kasa da Safayo na jihar, Alhaji Abduljabbar Umar Garko, ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a birnin Kano, inda ya ce wannan mataki na daga cikin shirin gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, na kyautata tsarin gudanarwa da samar da daidaito a cikin birni.
Kasuwar ‘Yan Lemo ta dade da zama cibiyar hada-hadar kayan marmari a Kano, inda ake saye da sayar da kayayyaki irin su lemo, abarba, gwanda, ayaba, kankana, mangwaro da sauransu.