Gwamnatin Bauchi ta kori jami’in ilimi bisa zargin lalata da mata

0
29

Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jihar Bauchi ta sanar da korar wani jami’in ilimi, Emos Joshua, malami a kwalejin Azare, bisa zargin cin zarafin mata.

Mai magana da yawun hukumar, Saleh Umar, ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne bayan jami’in ya karya dokoki na ma’aikatar jihar, musamman sashin 0327 (xxviii da xxix) na dokokin ayyukan gwamnati.

Umar ya kara da cewa an kammala ɗaukar dukkan matakan ladabtarwa kafin yanke wannan hukunci, kamar yadda dokar 0317 ta tanada.

Baya ga korar jami’in, hukumar ta kuma sanar da karin girma da sauye-sauye a ma’aikatar, inda wasu manyan jami’ai suka samu mukamai na wucin gadi. Haka kuma, an daukaka mukamin jami’an jinya 80 daga matakai daban-daban na aiki.

Shugaban hukumar, Ibrahim Muhammad, ya ce korar jami’in bai kasance hukunci kawai ba, illa mataki na kare mutunci da ingancin aikin gwamnati.

> “Wannan hukunci zai kasance izina ga sauran ma’aikata cewa bin ka’ida da kiyaye ladabi abu ne da ba za a yi sassauci a kai ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here