Kano: Gwamnati ta hana ƙarin kuɗin makarantu masu zaman kansu ba tare da izini ba

0
20

Gwamnatin Jihar Kano ta gargaɗi makarantun kuɗi da na sa-kai da su guji ƙara kuɗin makaranta ba tare da sahalewar hukuma ba.

Sakataren hukumar kula da makarantun kuɗi ta jihar, Malam Baba Umar, ya bayyana cewa dokar da aka kafa hukumar tun 2014 ta tanadi cewa dole sai gwamnati da ƙungiyar iyaye da malamai (PTA) sun amince kafin a yi duk wani ƙarin kuɗi.

Ya ce duk wata makaranta da ta karya wannan doka za ta fuskanci hukunci.

 Haka kuma ya gargadi masu makarantu da su daina tilasta wa iyaye sayen littattafai, kayan makaranta ko riga kai tsaye daga makarantu.

Baba Umar ya jaddada cewa ikon hukumar ba domin tsoratar da masu makarantu ba ne, sai dai don tabbatar da bin doka. Ya kuma shawarci iyaye da su bincika duk wani ƙarin kuɗi kafin su biya, tare da bin lokaci wajen biyan kuɗin makaranta domin sauƙaƙa gudanar da ayyukan makarantu yadda ya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here