Fitaccen masani kan tsaro, Dr. Audu Bulama Bukarti, ya yi watsi da ikirarin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, cewa gwamnatin tarayya na biyan kudin fansa tare da ba wa ‘yan bindiga abinci.
A yayin shirin Fashin Baki da ake yaɗawa kai tsaye, Bukarti ya bayyana cewa wannan zargi “ba gaskiya ba ne kuma yana da nasaba da siyasa.”
Ya ce babu wata doka ko manufofi da suka amince gwamnati ta rika tallafa wa ‘yan ta’adda, inda ya ƙara da cewa kudaden fansa da ake ji a kafofin watsa labarai yawanci iyalan mutanen da aka sace ne ko kuma al’umma ke tara su ba gwamnati ba.
Bukarti ya danganta matsalar tsaro da rashawa, yana mai cewa ita ce babbar hanyar da ke ƙarfafa ayyukan ta’addanci a Najeriya.
Game da tsarin rundunar soja, ya fayyace cewa shugaban ƙasa ne ke da ikon bayar da umarnin kai farmaki, ba gwamna ko minista ko kuma mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro ba.
Masanin kan tsaron ya jaddada cewa magance matsalar tsaro a Najeriya na buƙatar haɗin gwiwa tsakanin jama’a, gwamnati da hukumomin tsaro, tare da himma ta musamman wajen yaƙi da rashawa.