Najeriya Za Ta Gurfanar da Kwamandojin Ƙungiyar Ta’addanci Ta Ansaru

0
36

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta gurfanar da shugabanni biyu na ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru a gaban kotun tarayya dake Abuja a yau Alhamis.

Mutanen sune Mahmud Muhammad Usman, wanda ake kira Abu Bara’a/Abbas Mukhtar, da kuma mataimakinsa Abubakar Abba, wanda ake kira Isah Adam/Mahmud Al-Nigeri (Mallam Mamuda).

Za a gurfanar da su gaban Mai Shari’a Emeka Nwite bisa tuhume-tuhume guda 32 da suka shafi ta’addanci. Rahoton ya nuna cewa suna daga cikin wadanda suka kafa kuma suka shugabanci Jama’atu Ansarul Muslimeena Fii Bilaadis Sudan (Ansaru), wacce aka ayyana a matsayin haramtacciyar ƙungiya a Najeriya.

An cafke su ne tsakanin watan Mayu da Yuli 2025 a wani samame na musamman da jami’an tsaron leken asiri suka kaddamar. Mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ne ya sanar da hakan a ranar 16 ga watan Agusta.

Ƙungiyar Ansaru na daga cikin ƙungiyoyin da suka shahara wajen kai hare-hare da kuma yin garkuwa da mutane a sassa daban-daban na ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here