Gwamnatin tarayya zata karya farashin kayan abinci a faɗin Najeriya

0
55

Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakai na musamman domin rage tsadar kayan abinci, bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu.

Ƙaramin Ministan Harkokin Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja yayin wani taron horarwa ga manema labarai na majalisar dattijai.

Ya ce Shugaba Tinubu ya umurci kwamitin majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da ya gaggauta aiwatar da matakan da za su tabbatar da sauƙaƙe jigilar kayan gona.

Abdullahi ya ƙara da cewa shirin yana da alaƙa da hangen nesa na shugaban ƙasa na cimma dogaro da kai a fannin abinci, wanda ba wai kawai samarwa ba ne, har da sauƙin samu, arha, da kuma ingancin abinci.

A cewar sa, gwamnati za ta ƙaddamar da shirin kula da lafiyar ƙasar noma (Farmer Soil Health Scheme) da kuma gyara tsarin ƙungiyoyin haɗin gwiwa don ƙara ƙarfafa manoma a karkara.

“Shugaban ƙasa ya nuna babbar sha’awa ga ƙungiyoyin haɗin gwiwa a matsayin hanya ta samar da albarkatu, ƙirƙirar ayyukan tattalin arziki, da inganta rayuwar al’umma,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here