Matatar mai ta Dangote ta nesanta kanta daga rahoton da ke cewa za ta dakatar da aiki a sashen man fetur na tsawon watanni biyu zuwa uku.
Mai magana da yawun kamfanin, Anthony Chiejina, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya.
Wani rahoto da aka danganta ga wata jarida ya nuna cewa akwai yiwuwar sashen tace man fetur na masana’antar mai ganga dubu ɗari shida da hamsin a kowace rana ya tsaya, bayan zargin zubar wani sinadari tun daga ranar 29 ga watan Agusta.
Rahoton ya kuma ce akwai shirin sake fara aikin wani sashen tace mai a ranar 20 ga Satumba, amma gyare-gyare da maye gurbin kayan aiki na iya sa jinkirin komawa aiki har na tsawon watanni.
Sai dai Chiejina ya jaddada cewa wannan magana babu gaskiya a cikinta, inda ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da labaran ƙarya.