Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa talauci, rashin ayyukan yi, rashin makarantu, asibitoci da harkokin kasuwanci a karkara na daga cikin manyan dalilan da ke janyo matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya.
Ya bayyana haka ne a yayin taron kaddamar da littafin “Where I Stand” na marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi wanda Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya fassara shi zuwa harshen Larabci, wanda kungiyar JIBWIS ta shirya ranar Asabar.
Gwamna Sani wanda ya wakilci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wurin taron, ya gargadi ‘yan adawa da su daina siyasantar da batun tsaro ta hanyar ikirarin cewa za a iya murkushe ‘yan bindiga da makamai kawai.
A cewarsa, rikicin da ake fama da shi a Arewa maso Yamma ya sha bamban da na Boko Haram a Arewa maso Gabas saboda ba na akida ba ne, illa dai ya samo asali daga talauci da rashin kulawa da al’ummomin karkara.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa “ba za a iya magance matsalar tsaro da bindigogi kadai ba. Duk wanda ya ce hakan zai yiwu yana yuwa jama’a karya.”
Ya jaddada cewa duk da karuwar yawan jama’a a Najeriya cikin shekaru 45 da suka wuce, adadin sojojin kasar ya ragu daga 300,000 zuwa kasa da 250,000, abin da ya kara nuna rashin isassun jami’an tsaro a kasa.
Sani ya kara da cewa yawancin yankunan Zamfara, Birnin Gwari da Katsina babu jami’an tsaro, inda ake iya yin tafiyar kilomita 50 ba tare da ganin dan sanda ko soja ba.
Gwamna Sani ya jaddada cewa shugabanni da aka zaba su ne ke da alhakin kare jama’arsu, ba wai sai sun dogara kacokan ga shugaban kasa ko mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ba.
“Allah zai tambaye mu a lahira kan amanar da aka ba mu. Shi ya sa na zabi hanyar sulhu wajen magance matsalar tsaro a Jihar Kaduna,” in ji shi.