Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Kano ta sanar da rushewar Gadar Yaryasa da ke karamar hukumar Tudun Wada sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu a kwanakin nan.
Gadar dai na da matuƙar muhimmanci domin tana haɗa Kano da wasu jihohi kamar Kaduna, Plateau, Benue da kuma wasu jihohi.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Asabar, rundunar ta ce ta dauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
An sanya alamar gargadi a wurin tare da karkatar da ababen hawa.
Jami’an ’yan sanda na sashen MTD, tare da hadin gwiwar FRSC, KAROTA da ’yan kungiyar sufuri suna wajen domin kula da zirga-zirga.
An kuma kebe wurin gaba ɗaya domin kauce wa hadurra.
Rundunar ta roƙi direbobi da fasinjoji da ke tafiya ta Tudun Wada da su yi hakuri su kuma bin wasu hanyoyin da aka tanada.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya yi kira ga jama’a da su yi taka-tsantsan da kuma bin umarnin jami’an tsaro har sai an dauki matakan gyaran gada.
Sanarwar ta tabbatar da cewa za a rika baiwa jama’a ƙarin bayani idan akwai wani ci gaban da aka samu.