Zargin badaƙalar cin hanci ya ƙara zurfafa a gwamnatin Kano

0
33

Rahotanni sun bayyana cewa badakalar cin hanci da ta afka wa gwamnatin Jihar Kano ta ƙara zurfafa, bayan da kwamishinan ci gaban al’umma da yankunan karkara na jihar, Abdulkadir Abdulsalam, ya amsa cewa shi ne ya amince da biyan kudi har Naira biliyan 1.17 lokacin yana matsayin Akanta Janar na jihar. 

Hukumar ICPC ce ta bayyana cewa wannan biyan kudi na cikin wani zargin badakalar Naira biliyan 6.5.

A cewar takardun da ICPC ta samu, an yi biyan ne a watan Nuwamba 2023 domin wata kwangila da ba’a aiwatar ba. 

An kuma zargi Abdulsalam da haɗin baki da Abdullahi Rogo, babban daraktan protokol na Gwamna Abba Kabir Yusuf, wajen karkatar da kudaden jihar ta hannun ‘yan canji (BDC).

Hukumar ta gano cewa Abdulsalam ya yi amfani da takardun bogi na kamfanonin A.Y. Mai Kifi Oil and Gas Ltd. da kuma Ammas Petroleum Company Ltd., inda daga baya shugabannin kamfanonin suka ce sun sanya hannu ne bisa umarninsa, amma ba su da masaniya kan wata kwangila.

Binciken ya nuna cewa a ranar 9 ga Nuwamba 2023, an cire Naira biliyan 1.17 daga asusun jihar kai tsaye, aka mika shi ga wasu ‘yan canji, Gali Muhammad na Kazo Nazo da Nasiru Adamu na Namu Nakune. Daga nan ne aka ce Muhammad ya mika Dala miliyan a hannun Rogo a ofishin Kano da ke Asokoro, Abuja.

Duk da cewa Abdulsalam ya amsa cewa shi ne ya amince da biyan kudaden, bai iya bayyana dalilin da ya sa aka rika turawa kamfanonin canji kuɗin ba. Haka kuma bai amsa kiran waya da sakonnin PREMIUM TIMES don ya yi tsokaci kan lamarin ba.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here