Ƴan Najeriya zasu fara biyan gwamnatin Tinubu sabon harajin man fetur

0
27
Man fetur a Najeriya

Ƴan Najeriya zasu fara biyan gwamnatin Tinubu sabon harajin man fetur

Gwamnatin Tarayya ta sanya sabon haraji na kashi 5% kan kayayyakin man fetur, wanda zai fara aiki daga watan Janairu 2026, bisa ga sabuwar dokar haraji ta 2025 da Shugaba Bola Tinubu ya rattaba wa hannu a ranar 26 ga Yuni, 2025.

Sabon harajin zai shafi man fetur, dizal, da man jiragen sama, da sauran makamashin da ake sarrafawa daga mai da gas. Sai dai an ware gas ɗin girki, CNG da makamashin da ake sabuntawa daga wannan biyan haraji.

Idan farashin man fetur ya ci gaba da kasancewa a Naira 900 kowace lita, sabuwar dokar za ta sanya ’yan Najeriya su biya ƙarin Naira 45 kowace lita daga 2026.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here