Tinubu ya naɗa farfesa Yahaya Bunkure a matsayin shugaban Jami’ar Ilimi ta Zaria

0
36

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Farfesa Yahaya Bunkure a matsayin sabon Shugaban Jami’ar Ilimi ta Tarayya (Federal University of Education), Zaria, dake jihar Kaduna.

Mai ba wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa daya fitar a Abuja a yau Laraba.

Farfesa Bunkure, wanda kwararre ne a fannin kimiyya, a halin yanzu shi ne Shugaban Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, Kano.

A cewar sanarwar, shugaban ƙasa ya kuma naɗa Injiniya Abdurrazaq Nakore a matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwa (Pro-Chancellor) na Jami’ar Ilimi ta Tarayya Yusuf Maitama Sule, Kano. Hakazalika, ya naɗa Farfesa Abdullahi Kodage a matsayin Shugaban wannan jami’a.

Injiniya Nakore, wanda memba ne na Ƙungiyar Injiniyoyin Najeriya (NSE), ya taɓa riƙe mukamin Sakataren Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Karkara a jihar Jigawa.

Sanarwar ta kuma tunatar da cewa Jami’ar Ilimi ta Tarayya Zaria da ta Yusuf Maitama Sule, Kano, na daga cikin manyan Kwalejojin Ilimi guda huɗu da aka ɗaukaka matsayin su zuwa jami’o’i a shekarun 2022 zuwa 2023.

A bisa ƙa’ida, shugaban majalisar gudanarwa zai yi shekaru huɗu a kan mukami, yayin da shugabannin jami’a za su yi shekaru biyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here