Tinubu ya umarci a su sauya salon yaki da ’yan bindiga a Katsina

0
8
Tinubu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci rundunar sojoji da su sake fasalin dabarun yaki da ’yan bindiga a jihar Katsina ta hanyar amfani da na’urorin zamani wajen sanya ido da shawo kan matsalar tsaro.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, tare da wasu shugabannin jihar a fadar gwamnatin tarayya.

Tinubu ya jaddada cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa, tare da tabbatar da cewa al’umma sun samu cikakken tsaro.

“Za a ƙara daukar matakan tsaro na cikin gida, ciki har da yiwuwar kafa ’yan sandan jihohi da kuma ƙarfafa masu gadin daji,” in ji shi.

Ya kuma umarci hukumomin tsaro da su rika bayar da rahoton ayyukan su akai-akai daga Katsina, yana mai cewa:

“Dole ne mu kare rayuka, yara, wuraren ibada da kasuwanci. Ba za mu bari ’yan bindiga su ci gaba da tsoratar da mu ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here