Tinubu ya taya Shettima murnar cika shekaru 59 a duniya

0
37

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mataimakinsa, Kashim Shettima, murnar zagayowar ranar haihuwar sa inda ya cika shekaru 59, sannan ya yaba da kishin kasa, jajircewa da kuma amincin da ya nuna tun bayan fara tafiyar siyasar su tare.

A cikin saƙon taya murnar, Tinubu ya bayyana Shettima a matsayin amini kuma abokin tafiya na gaskiya wajen gina sabuwar Najeriya, tare da jaddada cewa ba ya yin nadamar zaɓar sa a matsayin mataimaki.

Shugaban ƙasar ya kuma yi nuni da irin gudunmawar Shettima tun daga lokacin da yake Gwamnan Jihar Borno da kuma Sanata, yana mai cewa ya nuna cewa jagoranci hidima ne, ba gata ba.

Tinubu ya ƙara da cewa haɗin gwiwar su ta haifar da nasarori a shirin Renewed Hope Agenda, wanda ya haɗa da haɓaka tsaro, inganta abinci da sauran su.

Ya roƙa wa Shettima ƙarin hikima, ƙarfi da kuma shekaru masu albarka a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here