Ƴan daba sun kaiwa tsohon ministan shari’a Abubakar Malami hari

0
15

Rahotanni sun bayyana cewa wasu matasa da ake kyautata zaton ’yan daba ne sun kai hari kan gungun motocin tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a Birnin Kebbi.

Lamarin ya faru ne a kan titin Old NITEL Road, jim kaɗan bayan Malami ya dawo daga gidan marigayi Malam Tukur Kola, babban limamin Masallacin Dr. Bello Haliru Jumu’ah, inda ya je yin ta’aziyya.

Shaidu sun ce ’yan daba sun yi amfani da duwatsu da makamai wajen lalata wasu daga cikin motocin dake cikin jerin motocin Malami.

Jami’an tsaro sun hanzarta zuwa wurin don kwantar da tarzoma, tare da tsare ofishin jam’iyyar APC mai mulki a jihar da kuma gidan Malami domin kare dukiyoyi da rayuka.

A wata sanarwa, kakakin jam’iyyar APC a jihar, Isa Abubakar As-Salafi, ya ce za a gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu a harin.

Shi kuwa Malami ya bayyana cewa abin takaici ne ganin yadda aka kai musu hari a lokacin da suka fito domin gaisuwar mutuwa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bello M. Sani, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa an fara bincike. Ya kuma gargadi jam’iyyun siyasa da shugabanninsu da su guji duk wani taro ko yaɗa manufofi da ka iya haddasa tashin hankali, kasancewar hukumar INEC bata bude lokacin yaƙin neman zaɓe ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here