Gwamnatin Kaduna ta zargi tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa’i, da ƙulla makirci na tayar da rikici ta hanyar “rigima, ruɗani da tunzura jama’a,” tare da gargadin cewa ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na jefa jihar cikin tashin hankali ba.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Dr. Suleiman Shuaibu, ne ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Litinin. Ya ce bayan faduwar abokan siyasar El-Rufa’i a zaɓen cike gurbi na ranar 16 ga Agusta, tsohon gwamnan ya ƙara daɗa ayyukan da ke barazana ga zaman lafiya da ci gaban jihar.
Shuaibu ya yi zargin cewa El-Rufa’i ya shirya wani “taron siyasa a ranar 30 ga Agusta wanda ya rikide ya zama tashin hankali, har da harbin bindiga da ya jefa rayukan jama’a cikin haɗari.
Haka kuma, gwamnatin jihar ta yi Allah-wadai da kalaman da El-Rufa’i ya yi a wani shirin talabijin, inda ya zargi gwamnati da bayar da rashawa ga ‘yan bindiga domin samun zaman lafiya.