Likitocin ƙasar nan sun saka lokacin shiga yajin aiki

0
21

Kungiyar Likitocin Masu Ƙwarewa ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwana goma don ta biya bukatun da suka jima suna nema, idan ba haka ba za ta tsunduma yajin aiki a duk faɗin ƙasar nan.

Sanarwar hakan ta fito ne daga shugabancin kungiyar bayan taron gaggawa na majalisar zartarwa ta ƙasa da aka gudanar ta hanyar yanar gizo a ranar Lahadi.

Daga cikin koke-koken da kungiyar ta lissafo akwai rashin biyan kuɗin horon likitoci masu neman kwarewa na shekarar 2025, jinkirin biyan bashin albashi musamman na karin kaso ashirin da biyar da kaso talatin da biyar a tsarin sabon albashi na likitoci, da kuma biyan bashin kudin kayan aiki na shekarar 2024.

Kungiyar ta kuma bukaci hukumar kula da likitoci da likitocin hakora ta Najeriya da ta dawo da amincewa da takardun shaidar kwarewar likitoci na yammacin Afirka. Haka kuma ta bukaci cibiyar koyar da manyan likitoci ta Najeriya da ta daina jinkirin bayar da takardun shaidar kwarewa ga waɗanda suka cancanta.

A matakin jihohi kuwa, kungiyar ta yi kira ga gwamnatocin Kaduna da Oyo da su gaggauta warware matsalolin walwalar likitocin masu neman kwarewa a jihohinsu.

Kungiyar ta gargadi cewa idan gwamnati ta gaza biyan wadannan bukatu kafin karewar wa’adin da aka sanya, ba ta da wani zaɓi illa ta tsunduma yajin aiki a faɗin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here