Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da kama mutum 107 a watan Agusta bisa laifuka daban-daban da suka haɗa da fashi da makami, garkuwa da mutane, fataucin mutane da miyagun ƙwayoyi da kuma sata.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin, inda ya ce an kwato bindiga AK-47 guda ɗaya, bindigogi na gida guda bakwai, harsasai 11, motoci, babura, shanu, takubba, wukake da kuma tarin miyagun ƙwayoyi.
Ya bayyana cewa nasarorin sun samu ne ta hanyar sabon shirin tsaro mai suna Operation Kukan Kura, wanda ke haɗa dabarun zamani da haɗin gwiwar al’umma.
Haka kuma ya ce an fara amfani da kayan aikin zamani wajen gano laifuka, lamarin da ya taimaka wajen samun nasarar.
Bakori ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da rahoto kan duk wani abin da suka gani da ke da alaƙa da aikata laifi, ta hanyar ofisoshin ‘yan sanda ko layin gaggawa na rundunar.