Atiku Ya Yi Kira Da a Soke Zaɓen Ƙananan Hukumomi a Rivers

0
12

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci a soke sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar Rivers, yana mai kiran zaɓen “abin kunya da cin fuskar tsarin dimokraɗiyya.”

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, Atiku ya zargi jam’iyyar APC da “shirya keta doka don cimma nasara ta siyasa.”

“Ina kira ga ‘yan Najeriya, ƙungiyoyin duniya da abokan hulɗa su lura da yadda gwamnatin Tinubu ke ƙoƙarin karkatar da ƙasar zuwa turba mai haɗari,” in ji shi.

Ya kuma roƙi jam’iyyun adawa a jihar su ƙi amincewa da sakamakon da aka bayyana, yana mai cewa “gwamnatin ba ta da hurumin gudanar da zaɓen.”

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC) ta sanar da cewa jam’iyyar APC ce ta lashe ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23, yayin da PDP ta samu sauran guda uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here